
Kasuwanci
Podcast af RFI
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.
Begrænset tilbud
3 måneder kun 9,00 kr.
Derefter 99,00 kr. / månedIngen binding.
Alle episoder
114 episoder
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan mako tare da Ahmad Abba ya yi dubi ne kan hada-hadar baje koli da ta gudana a jihar Kano dake arewacin tarayyar Najeriya, bukin na karo na 40 da ake shiryawa kan janyo hankulan yan kasuwa daga ciki da wajen Najeriya musamman ma makwabtan kasashe.Inda a wannan karo rundunar sojin Najeriya ma ta baje kolinta a kasuwar.

Shirin Kasuwa a kai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abbab ya yi nazari game da tabbacin gano man fetur da iskar gas a arewacin Najeriya.

Kungiyar Kwadagon Ghana GHUTA ta sanar da shirin ta na gudanar da gagarumin aikin rufe shagunan ‘yan kasashen waje da ke birnin Accra. Lamarain da ya samo asali yau da shekaru kusan 20 a kasar ta Ghana. Abdoulaye Issa da ya ziyarci kasar ta Ghana ya jiyo ta bakin wasu yan kasuwa da wakilan kungiyar ta Ghuta a Ghana.

A jahar Borno dake Nigeria an samu iftilian Gobara daya kona kasuwar waya da aka fi sani da kasuwar jagol dake postoffice a tsakiyar Birnin Maiduguri, wannan ya gurgunta tattalin arzikin wanna yanki ganin cewa wanna yankin na fama da matsalar tsaro wadda aka shafe fiye da shekara 10, inda mutane fiye da milyan 2 rikicin Boko Haram ya raba su da matsugunin su. Sai dai gwamnatin jahar ta talafawa waddan nan matasa yan kasuwa da naira milyan 60 domin rage musu asara da sukayi da kuma sama musu wani wuri na musaman.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da daukar matakai na fadakar da jama’a domin gujewa sayar da filaye a wasu yankunan arewacin kasar, yankunan da ake sa ran soma fitar da mai. a wani mataki da ake ganin watakila zai iya fidda wannan bangare na Najeriya kunya. Ahmad Abba a cikin shirin kasuwa a kai miki dole ya duba alfanun mataki.
Begrænset tilbud
3 måneder kun 9,00 kr.
Derefter 99,00 kr. / månedIngen binding.
Eksklusive podcasts
Uden reklamer
Gratis podcasts
Lydbøger
20 timer / måned