Muhallinka Rayuwarka
Podcast by RFI
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanay...
Start 7 days free trial
After trial, only 79,00 kr. / month.Cancel anytime.
All episodes
98 episodesMatsalar kashe jakuna ta zama babbar barazana ga yawan jakuna da ake dasu a Duniya inda masana ke cewa idan ba’a dauki matakin da ya dace ba, ana iya rasa kusan rabi na jakunan nan da shekaru 5. Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da Najeriya ke shirin yin doka kan haramta kashe jakuna, yayin da kungiya mai suna Donkey Sanctuary ta kaddamar da rahoto kan hakan a Abuja dake Najeriya. A cikin shirin Bashir Ibrahim Idris ya duba irin matsalolin da ake fuskanta a wasu yankunan kasashen Afrika.
shirin Muhallinka Rayuwarka yana nazari ne kan al’amuran da suka shafi noma da kiwo, canji da kuma dumamar yanayi da dai sauran batutuwan da suka shafi Muhalli. A yau shirin zai mayar da hankali ne kan cece kucen da ake ci gaba da yi game da matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya na rufe iyakokin ta dake kan tudu domin hana shigar da shinkafa cikin kasar daga waje. Cikin shirin zaku ji yadda aka tafka muhawara tsakanin masu rajin kare hakkin jama’a da masana a fannin noman da kungiyar manoman shinkafa da kuma kananan manoman dake a matsayin jigon wannan tsari.
Shirin rayuwarka muhallinka na wannan makon ya halarci taron koli kan harakar noma a nahiyar Afrika wanda Najeriya ta karbi bakuncin sa a birnin Abuja. Nura Ado Suleiman ya samu tattaunawa da masana harakar noma a cikin shirin.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan karo yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda mazauna wani kauye da ake kira da Kwangwame dake karamar hukumar Takeita a Jahar Damagaram, suka yi namijin yunkuri don kare Hamada dake barazana ga dajin yankin da suke.
A cikin shirin rayuwarka muhalinka ,Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali zuwa rahoto dake nuna cewa nan da yan shekaru mudin ba a dau matakan magance matsalar abinci a Najeriya. A cikin shirin ya samu tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki a Duniyar noma.
Available everywhere
Listen to Podimo on your phone, tablet, computer or car!
A universe of audio entertainment
Thousands of audiobooks and exclusive podcasts
No ads
Don't waste time listening to ad breaks when listening to Podimo's content.
Start 7 days free trial
After trial, only 79,00 kr. / month.Cancel anytime.
Exclusive podcasts
Ad free
Non-Podimo podcasts
Audiobooks
20 hours / month