
hausa
Nyheder & politik
Begrænset tilbud
Derefter 99 kr. / månedOpsig når som helst.
Læs mere Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Muhallinka Rayuwarka - Haramta cinikin jakuna a Duniya
Matsalar kashe jakuna ta zama babbar barazana ga yawan jakuna da ake dasu a Duniya inda masana ke cewa idan ba’a dauki matakin da ya dace ba, ana iya rasa kusan rabi na jakunan nan da shekaru 5. Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da Najeriya ke shirin yin doka kan haramta kashe jakuna, yayin da kungiya mai suna Donkey Sanctuary ta kaddamar da rahoto kan hakan a Abuja dake Najeriya. A cikin shirin Bashir Ibrahim Idris ya duba irin matsalolin da ake fuskanta a wasu yankunan kasashen Afrika.
Muhallinka Rayuwarka - Muhawara dangane da batun rufe kan iyakar Najeriya da wasu kasashe
shirin Muhallinka Rayuwarka yana nazari ne kan al’amuran da suka shafi noma da kiwo, canji da kuma dumamar yanayi da dai sauran batutuwan da suka shafi Muhalli. A yau shirin zai mayar da hankali ne kan cece kucen da ake ci gaba da yi game da matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya na rufe iyakokin ta dake kan tudu domin hana shigar da shinkafa cikin kasar daga waje. Cikin shirin zaku ji yadda aka tafka muhawara tsakanin masu rajin kare hakkin jama’a da masana a fannin noman da kungiyar manoman shinkafa da kuma kananan manoman dake a matsayin jigon wannan tsari.
Muhallinka Rayuwarka - Taron koli kan noma a Afrika
Shirin rayuwarka muhallinka na wannan makon ya halarci taron koli kan harakar noma a nahiyar Afrika wanda Najeriya ta karbi bakuncin sa a birnin Abuja. Nura Ado Suleiman ya samu tattaunawa da masana harakar noma a cikin shirin.
Muhallinka Rayuwarka - Nijar: An karrama al'ummar Kwangwame saboda yakar Hamada
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan karo yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda mazauna wani kauye da ake kira da Kwangwame dake karamar hukumar Takeita a Jahar Damagaram, suka yi namijin yunkuri don kare Hamada dake barazana ga dajin yankin da suke.
Muhallinka Rayuwarka - Yunkurin samar da hanyoyi don magance matsalar yunwa a Najeriya
A cikin shirin rayuwarka muhalinka ,Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali zuwa rahoto dake nuna cewa nan da yan shekaru mudin ba a dau matakan magance matsalar abinci a Najeriya. A cikin shirin ya samu tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki a Duniyar noma.
Vælg dit abonnement
Begrænset tilbud
Premium
20 timers lydbøger
Podcasts kun på Podimo
Gratis podcasts
Opsig når som helst
1 måned kun 9 kr.
Derefter 99 kr. / måned
Premium Plus
100 timers lydbøger
Podcasts kun på Podimo
Gratis podcasts
Opsig når som helst
Prøv gratis i 7 dage
Derefter 129 kr. / month
1 måned kun 9 kr. Derefter 99 kr. / måned. Opsig når som helst.